Home AFRICA Buhari Ya Amince Da Kafa ‘Yan Sandan Unguwanni – IG

Buhari Ya Amince Da Kafa ‘Yan Sandan Unguwanni – IG

3 min read
Comments Off on Buhari Ya Amince Da Kafa ‘Yan Sandan Unguwanni – IG
0
71

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa ‘yan sandan unguwanni a matsayin wata mataki na magance karuwar barazanar tsaro da ake kara samu a sassan Najeriya a cewar Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya.

Sufeta Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu ya bayar da wannan sanarwar ne a ranar Talata a wurin taron Shugabanin Gargajiya na Arewa da aka gudanar a Kaduna.

Mahalarta taron sun tattauna muhimman batutuwa ne da suka shafi tsaro musamman a Arewacin kasar.

Mataimakin shugban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya za ta fitar da sabuwar tsari na ‘yan sandan unguwanni domin inganta harkokin tsaro.

Osinbajo ya ce wannan za ta zama shimfida ga sabuwar tsarin aikin ‘yan sanda a Najeriya.

Ya bayar da tabbacin cewa kafa ‘yan sandan unguwani ba zai rage wa jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya ikon su ba.

A jawabin da ya yi a wurin taron a Kaduna, Sufeta Janar na ‘yan sandan ya ce rundunar ta samu nasarori masu yawa wurin kare afkuwar laifuka da barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma a kwanakin nan.

Mista Adamu ya ce an kara samun nasarorin sosai tun bayan kaddamar da atisayen ‘Operation Puff Adder’.

“Sabon tsarin ‘yan sandan unguwani zai inganta samar da tsaro a tsakanin al’umma tare da magance barazana ga tsaro,” inji shi.
IG din ya ce Najeriya ta kwakwayo wannan tsari ne daga kasar Ingila inda ake amfani dashi domin inganta tsaro.

Za a tsara shirin yadda zai dace da irin hanyoyin samar tsaro na gargajiya ya ke a Arewacin Najeriya.

“Za a zabo jami’an tsaron ne daga cikin mazauna unguwani domin su bayar da gudunmawa inda za suyi aiki karkashin rundunar ‘yan sandan Najeriya.

“Za a kaddamar da wannan sabuwar tsarin ne bisa umurnin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, babban kwamandan hafsoshin Najeriya” inji shi.

Comments

0 comments

Load More Related Articles
Load More By administrator
Load More In AFRICA
Comments are closed.

Check Also

The president is not in charge of this nation – Wole Soyinka says

Nobel laureate, Wole Soyinka, says he does not believe President Buhari is the one in char…